Rikicin manoma da makiyaya zai iya shafar zaben 2019 – Kungiya

Rikicin manoma da makiyaya zai iya shafar zaben 2019 – Kungiya

Wani sabon rahoto ya nuna cewa an rasa rayukan mutane fiye da 1, 300, yayin da wasu mutum dubu 300 kuma suka rasa muhallansu a cikin shekarar nan kadai a sakamakon rikicin manoma da makiyaya a kasar.

Wata kungiya mai suna The International Crisis Group, ta ce rikicin zai iya shafar zabuka da za’a gudanar a 2019.

A cewar kungiyar ta ce zai yi wuya ace an wuce kwana guda ba tare da an samu labari akan rikicin manoma da makiyaya a kasar ba, sai dai yana da wuya a tantance sahihan bayanai na asarar da ake yi.

Rikicin manoma da makiyaya zai iya shafar zaben 2019 – Kungiya

Rikicin manoma da makiyaya zai iya shafar zaben 2019 – Kungiya

Kungiyar ta ce rikicin ya samo asali ne daga wasu manyan matsaloli da suka hada da sauyin yanayi da karin bukatuwar filin noma.

KU KARANTA KUMA: Atiku yayiwa Samuel Ortom maraba da dawowa PDP

Amma ta ce rikicin ya ta'azzara ne a 2018. saboda yawaitar kungiyoyin kabilu masu dauke da makamai.

Sannan kuma ta dora alhaki a kan gwamnati na rashin hukunta masu laifi, da bullo da dokar hana kiwo wadda makiyaya ke adawa da ita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel