Kwan gaba kwan baya: Wasu Sanatocin zasu sake komawa APC bayan ficewarsu

Kwan gaba kwan baya: Wasu Sanatocin zasu sake komawa APC bayan ficewarsu

- Guguwar sauya sheka har yanzu dai bata lafa a siyasar Najeriya ba

-Da alamu wasu 'yan majalisun na iya sake komowa jam'iyyar APC bayan sun fice dafa cikinta

- Wannan na zuwa kasa da kwanaki biyu da ficewarsu daga jam'iyyar ta APC mai mulki

Shugaban mafi rinjaye na majalisar datijjai Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa dukkan wadanda suka fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP zasu dawo cikin jam'iyyar kafin zaben shekara ta 2019.

Da yiwuwar fusatattun ‘yan majalisar da suka sauya sheka suka komo APC – Sanata Ahmed Lawal

Da yiwuwar fusatattun ‘yan majalisar da suka sauya sheka suka komo APC – Sanata Ahmed Lawal

Gidan Talabijin na Channels ya bayyana cewa, shugaban masu rinjayen ya shaida hakan ne jim kadan bayan tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fada shugaban kasa dake Aso Rock.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Sanatocin na tsawon mintuna 30 wanda Sanata ya shaida cewa a majalisar har yanzu APC ce ke da rinjaye da ‘yan majalisu 53, yayinda PDP take da da ‘yan majalisu 48, sai jam'iyyar ADC da take da guda 2.

Lawan ya shaida cewa bayan sa'o'i 24 wasu daga cikin wadanda suka sauya shekar daga jam'iyyar ta APC sun yi nadama kuma suna masu nuna sha'awarsu wajen ganin sun dawo.

Haka kuma Sanatan yayi kira ga wasu masu ruwa da tsaki a majalisar da su dawo jam'iyyar ta APC.

KU KARANTA: A karshe APC tayi magana kan ficewar gwamnan Benuwe daga jam’iyyar

Shi ma daga nasa bangarensa Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya wanda ya samu halartar taron, amma sai dai ya ce har ya zuwa yanzu bai gama saukowa daga fushin da yayi da jam’iyyar ba.

Da yiwuwar fusatattun ‘yan majalisar da suka sauya sheka suka komo APC – Sanata Ahmed Lawal

Da yiwuwar fusatattun ‘yan majalisar da suka sauya sheka suka komo APC – Sanata Ahmed Lawal
Source: Depositphotos

Amma sai dai tabbas ya aminta da yanayin shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin Adams Oshiomhole, inda yace yana da yakinin zai kawo karshen matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta.

Shi ma daga bangarensa shugaban jam'iyyar ta APC ya ce babu wani da zai tunzura jam'iyyar ko shugaba Buhari wajen hana su cikawa talakawa alkawarikansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel