Zalunci: Hukuma ta damke wata mata da ta yiwa karamar yarinyan dukan tsiya kan karamin laifi (Kalli hotunan)

Zalunci: Hukuma ta damke wata mata da ta yiwa karamar yarinyan dukan tsiya kan karamin laifi (Kalli hotunan)

A jiya Laraba, 25 ga watan Yuli ma’aikatar harkokin mata na jihar Kaduna ta mika wata yarinya mai suna Zahra ga mahaifinta wanda ya taso daga Maiduguri zuwa Kaduna.

Hakan ya faru ne sanadiyar irin zaluncin da wacce aka ba rainon yarinyar ke mata a jihar Kaduna.

Wacce aka baiwa rainonta mai suna Ramatu, ta yiwa Zahra mugun duka saboda ta yi kasha kan gado. Wannan abu ya tayar da hankulan jama’a wanda ya sanya aka kwace yarinyar aka kaita ma’aikatar harkokin matan jihar.

Zalunci: Hukuma ta damke wata mata da ta yiwa karamar yarinyan dukan tsiya kan karamin laifi (Kalli hotunan)

Zalunci: Hukuma ta damke wata mata da ta yiwa karamar yarinyan dukan tsiya kan karamin laifi (Kalli hotunan)

A rahoton da muka samu daga ma’aikatar, sun bayyana yadda abin ya faru. Suka ce: "An kawo Zhahra ma’aikatar harkokin matan jihar Kaduna a wani irin yanayi mara dadi. Yar uwarta ta yi mata dukan tsiya saboda tayi kasha kan gado. Da wuri ma’aiktar ta dau matakin kula da yarinyar.”

Zuwa yanzu hukumar yan sanda sun damke Ramatu, wacce ke rainon Zahra kuma za’a gurfanar da ita a kotu ba da dadewa ba. Babu wani dalilin da zai sa ayiwa yaro irin wannan zalunci.”

Zalunci: Hukuma ta damke wata mata da ta yiwa karamar yarinyan dukan tsiya kan karamin laifi (Kalli hotunan)

Zalunci: Hukuma ta damke wata mata da ta yiwa karamar yarinyan dukan tsiya kan karamin laifi (Kalli hotunan)

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel