Ba zan taba tsoma hannu cikin makircin tsige Saraki ba - Shehu Sani

Ba zan taba tsoma hannu cikin makircin tsige Saraki ba - Shehu Sani

Shehu Sani, sanata mai wakiltan yankin kaduna ta tsakiya, yace baya cikin wadanda ke shirya makarkashiya don tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Sani yace mutane suyi watsi da zance domin wasu 'yan adawa ne kawai ke yi masa sharri. Ya kara da cewa akwai kyakyawar dangantaka tsakaninsa da shugaban majalisar kuma zai cigaba bashi goyon baya.

Shehu Sani yace an janyo hankalinsa kan rahoton da wata kafar yadda labarai na yanan gizo mara tushe ta wallafa inda tace shi (Shehu Sani), da wasu sanatoci suna shirye-shiryen tsige shugaban majalisa Bukola Saraki a ranar Talata 24 ga watan Yulin shekarar 2018.

Ba zan taba tsoma hannu cikin makircin tsige Saraki ba - Shehu Sani

Ba zan taba tsoma hannu cikin makircin tsige Saraki ba - Shehu Sani

KU KARANTA: Wani ya yiwa mahaifiyarsa yankan rago saboda ya gaji filayenta

Sanatan yace bashi da masaniya a kan afkuwar lamarin kuma idan da gaske an shirya wani abu mai kaman haka, ya yi tir da wadanda suka shirya makircin. Yace ba zai taba saka hannu cikin yunkurin tsige Saraki ba saboda babu dalilin aikata hakan a yanzu.

"Akwai kyakyawar alaka tsakani na da Saraki tun shekarar 2015 kuma ya kasance yana taimaka min a lokutan da na samu kaina cikin mawuyacin hali kuma nima nakan taimaka masa idan nasa ya taso.

"Ya kasance yana jogorancin majalisar da dattaku kuma ya na mutunta ra'ayoyi na ko a lokutan da muke samu banbancin ra'ayoyi. Shugaban majalisa Saraki da Ekweremadu suna gudanar da ayyukansu yadda ya dace." inji Sani.

Shehu Sani yace wadanda ke yadda labarin suna bata lokacinsu ne kawai domin sharrin da suke nufinsa dashi ba za tayi tasiri ba.

"Zan cigaba da bawa Saraki da Ekweremadu goyon baya a matsayinsu na shugabanin majalisa har zuwa lokacin da zan bar majalisar. Kuma ra'ayina ne zabar jam'iyyar da zan shiga."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel