Atiku yayiwa Samuel Ortom maraba da dawowa PDP

Atiku yayiwa Samuel Ortom maraba da dawowa PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuli yayiwa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom maraba da dawowa jam’iyyar Peoples Democratic Party, bayan sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress.

Atiku ya wallafa a shafinsa na twitter cewa ja’iyyar PDP zata yiwa mutanen jihar Benue aiki mafi inganci.

“Ya kai Gwamna Samuel Ortom maraba da dawowa gida zuwa @OfficialPDPNig, jam’iyya mai wanzar da daidaito, adalci da zai yi aiki mafi inganci ga mutanen Benue.”

Atiku yayiwa Samuel Ortom maraba da dawowa PDP

Atiku yayiwa Samuel Ortom maraba da dawowa PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci dukkanin mambobinta dake jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da su dawo gida sannan su ceto kasar.

KU KARANTA KUMA: Masu sauya sheka za su rasa kujerunsu a 2019 kuma Saraki ba zai iya cetonsu ba – Sanata Ibrahim

Jam’iyyar ta yi wannan roko ne a wata sanarwa daga sakataren labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan, a ranar Laraba jim kadan bayan gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar adawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel