Da duminsa: Shugaba Buhari ya isa dira jihar Kaduna

Da duminsa: Shugaba Buhari ya isa dira jihar Kaduna

Rahoton da muke samu na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Kaduna a yau Alhamis, 26 ga watan Yuli 2018.

Shugaba Buhari ya tafi Kaduna ne domin halartan taron yaye manyan jami'an sojin Najeriya na kashi 40 a makarantan jami'an soji da ke garin Jaji, jihar Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tarbi shugaban kasa ne yayinda ya shigo jihar kuma zai rakasa taron a garin Jaji.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya isa dira jihar Kaduna

Da duminsa: Shugaba Buhari ya isa dira jihar Kaduna

Shugaba Buhari ya tafi Kaduna ne bayan ganawa da sanatocin jam'iyyar APC da suka rage a majalisar dattawa bayan guda 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyun adawa na PDP da ADC.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta hada gwiwa da kamfanonin Fasahar zamani domin yakar labaran bogi

Daya daga cikin sanatocin da ake sa ran zai tafi, Sanata Shehu Shehu, ya canza ra'ayinsa game da shugabancin jam'iyyar inda yace abubuwan da ya sa yake kokarin barin jam'iyyar, an fara shawo kansu.

Amma duk da haka gwamnan jihar Kaduna wanda sukayi hannun riga da sanatan ya ce ba zai yi sulhu da yan tawaye ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel