Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da Dino Melaye

Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da Dino Melaye

Rahottani da muka samu sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun sace Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi ta yamma a garin Abuja.

Kamar yadda Sanata Ben Murray Bruce ya rubuta a shafinsa na Twitter, 'yan bindigan sun tare tawagar Dino Melaye ne a safiyar yau Alhamis a Gwagwalada dake Abuja.

Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da Dino Melaye

Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da Dino Melaye

Majiyar Legit.ng ta gano cewa Melaye yana hanyarsa ta zuwa jihar Kogi ne don ya amsa gayyatar da kotun majistare dake jihar tayi masa.

KU KARANTA: Fashin Offa: Ministan shari'a Malami ya wanke Saraki

Dino Melaye yana daya daga cikin Sanatocin da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a cikin wannan makon.

A yanzu dai ba'a san inda Sanatan yake ba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel