Gwamnatin Tarayya ta hada gwiwa da kamfanonin Fasahar zamani domin yakar labaran bogi

Gwamnatin Tarayya ta hada gwiwa da kamfanonin Fasahar zamani domin yakar labaran bogi

Gwamnatin tarayya ta hada gwiwa da wasu manyan kamfanoni sada zumunta musamman Google, Facebook, WhatsApp da sauran su domin ribatar albarka fasahar su ta zamani domin yaki da yaduwar labarai na bogi a shaci fadi.

Ministan Labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammad, shine ya bayyana hakan a taron ganawa da masu ruwa da tsaki kan rawar da dandalan sada zumunta ke takawa wajen yaduwar labaran bogi da aka gudanar a jihar Legas.

Yake cewa, dole ne Najeriya tayi nasara akan yaki da yaduwar labaran bogi kasancewar ta kasa mai kunshe da mutane masu al'adu da addinai daban-daban da labaran bogi ke haddasa rikici da tarzoma.

Gwamnatin Tarayya ta hada gwiwa da kamfanonin Fasahar zamani domin yakar labaran bogi

Gwamnatin Tarayya ta hada gwiwa da kamfanonin Fasahar zamani domin yakar labaran bogi

Sai dai Ministan ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ba za ta yiwa al'ummar kasar nan ta karfi ba wajen cimma manufar da ta sanya a gaba domin kuwa yana da tabbacin cewa akwai wadatattun dokoki da tsare-tsare da za su tabbatar da hakan a kasar nan.

KARANTA KUMA: Abinda ya sanya Hukumar 'yan sanda ta bukaci na gabatar da kaina - Saraki

A sanadiyar haka Ministan yake kira ga daukacin al'ummar kasar nan wajen yakar wannan annoba tare da tsarkake ta.

Ya kara da cewa, kasashe da kungiyoyi duniya da dama sun daura damara tare da aiwatar da shirye-shirye domin yaki da yaduwar labarai na bogi da shaci fadi sakamakon barazanar zagon kasa da yake tattare da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel