Ku dawo gida – PDP ga sauran tsoffin ‘ya’yanta bayan sauya shekar Ortom

Ku dawo gida – PDP ga sauran tsoffin ‘ya’yanta bayan sauya shekar Ortom

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci dukkanin mambobinta dake jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da su dawo gida sannan su ceto kasar.

Jam’iyyar ta yi wannan roko ne a wata sanarwa daga sakataren labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan, a ranar Laraba jim kadan bayan gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar adawa.

Sun yi maraba da gwamnan sannan sun yaba masa akan nuna karfin gwiwa da isa a wannan lokaci mai wuyar sha’ani.

Ku dawo gida – PDP ga sauran tsoffin ‘ya’yanta bayan sauya shekar Ortom

Ku dawo gida – PDP ga sauran tsoffin ‘ya’yanta bayan sauya shekar Ortom
Source: Depositphotos

PDP ta kuma jinjinawa gwamna Ortom kan jajircewa akan mutanen Benue da kuma bashi tabbacin cewa zai samu cikakken yanci kamar ko wani dan jam’iyya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce yiwuwar sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na da karfi sosai.

KU KARANTA KUMA: Masu sauya sheka za su rasa kujerunsu a 2019 kuma Saraki ba zai iya cetonsu ba – Sanata Ibrahim

A cewar jaridar Daily Trust, shugaban majalisar dattawan ya fadi hakan ne ga Reuters a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli.

Furucin Saraki na zuwa ne yan kwanaki bayan sanatocin APC 14 sun bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP da ADC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel