Fashin Offa: Ministan shari'a Malami ya wanke Saraki

Fashin Offa: Ministan shari'a Malami ya wanke Saraki

- Ministan shari'a, Abubakar Malami, yace hukumar 'yan sanda bata da hujjoji da zata alakanta Saraki da fashin Offa

- Malami ya kuma wanke gwamnan jihar Kwara, Abdulfattah Ahmed daga zargin da ake masa na hannun cikin fashin

- Ministan yace mutane shiddan da aka kama da hannu dumu-dumu cikin fashin ne ya kamata a gurfanar gaban kotu

Ministan sharia'a na kasa, Abubabar Malami, ya shaidawa hukumar 'yan sanda cewa babu wata sahihiyar hujja da ta alakanta shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed da fashin banki da akayi a Offa inda kimanin mutane 31 suka rasa rayyukansu.

Fashin Offa: Ministan shari'a Malami ya wanke Saraki

Fashin Offa: Ministan shari'a Malami ya wanke Saraki

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, Mr Malami ya aike wa hukumar 'yan sanda wasika a ranar 22 ga watan Yuni inda ya bukaci su sake fadada bincikensu kafin ambatan shugaban majalisar a matsayin wanda ake zargi kafin ma ayi maganar gurfanar dashi.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

Kazalika, an kuma wanke shugaban ma'aikata na gwamnan jihar Kwara da ake zargi da hada baki da wadanda ake tuhuma da aikata fashi da makamin. Lauya mai shigar da kara yace "babu gamsasun hujjoji da za'ayi amfani dasu wajen gurfanar dashi gaban kotu."

Ofishin ministan shari'a tace mutane shiddan da aka samu da hannu dumu-dumu ne kawai ya kamata a gurfanar gaban kotu bisa laifin fashi da makami inda ya kara da cewa inda aka tabbatar da sun aikata laifin ana iya yanke musu hukuncin kisa.

A daren Litinin, Mr Saraki yace wasikar da ministan shari'a ya aike wa 'yan sandan hujja ce dake nuna cewa babu wata dalilin da zai sa ya amsa gayyatar da 'yan sanda su kayi masa a safiyar Talata saboda ministan shari'a ya riga ya wanke shi daga dukkan zargin hannu a fashin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel