Masu sauya sheka za su rasa kujerunsu a 2019 kuma Saraki ba zai iya cetonsu ba – Sanata Ibrahim

Masu sauya sheka za su rasa kujerunsu a 2019 kuma Saraki ba zai iya cetonsu ba – Sanata Ibrahim

Sanata Abu Ibrahim wadda ya kasance shugaban kwamitin lamuran yan sanda a majalisar dattawa ya bukaci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da su yi murabu daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar TheNation ta rahoto cewa sanatan yankin Katsina ta kudu yayi ikirarin cewa akwai wani shiri da masu sauya shekar APC ke yi don tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce Saraki ba zai ceci sanatocin da suka bar APC ba idan lokacin yin hakan ya taso.

Masu sauya sheka za su rasa kujerunsu a 2019 kuma Saraki ba zai iya cetonsu ba – Sanata Ibrahim

Masu sauya sheka za su rasa kujerunsu a 2019 kuma Saraki ba zai iya cetonsu ba – Sanata Ibrahim

Ibrahim ya bayyana cewa sauya sheka ba zai shafi farin jinin APC a 2019 ba.

KU KARANTA KUMA: Yiwuwar barina APC na da karfi sosai - Saraki

A halin da ake ciki, Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce yiwuwar sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na da karfi sosai.

A cewar jaridar Daily Trust, shugaban majalisar dattawan ya fadi hakan ne ga Reuters a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli.

Furucin Saraki na zuwa ne yan kwanaki bayan sanatocin APC 14 sun bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP da ADC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel