Ya yiwa mahaifiyar sa yankan rago saboda abincin karin kumallo

Ya yiwa mahaifiyar sa yankan rago saboda abincin karin kumallo

A ranar Larabar nan ne wani mutum wanda ba a bayyana sunan sa ba ya kashe mahaifiyar sa, saboda sun samu rashin jituwa akan abincin karin kumallo

Ya yiwa mahaifiyar sa yankan rago saboda abincin karin kumallo

Ya yiwa mahaifiyar sa yankan rago saboda abincin karin kumallo

A ranar Larabar nan ne wani mutum wanda ba a bayyana sunan sa ba ya kashe mahaifiyar sa, saboda sun samu rashin jituwa akan abincin karin kumallo.

Wani mutum shima wanda ya nemi a boye sunan sa, yayi magana da wakilan mu, cewar gardama ta barke a tsakanin mahaifiyar da yarontan, inda mahaifiyar ta ce ita doya take so, shi kuma yaron yace taliya yake so.

DUBA WANNAN: Yanzu - yanzu: Buhari sunyi ganawar sirri da Babban Sufeton 'Yan Sanda

Mutumin yace gardamar tayi karfi a tsakanin su, inda mahaifiyar ta nace akan doya zata yi a matsayin abincin karin kumallon. Basu jima suna musun ba kafin mu isa wurin, muka tarar da Dan ya kashe mahaifiyar tashi, ya barta cikin jini.

Ba jimawa aka sanar da hukumar ‘yan sanda, inda wani yake bayyanawa hukumar cewar dama yaron suna da dan matsala tsakanin sa da mahaifiyar tasa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mr Harun Mohammed, ya ce zai binciko musabbabin kisan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel