Abin da Jami’an tsaro su kayi wa Bukola Saraki da Ekweremadu bai dace da tsarin kasa ba – Shehu Sani

Abin da Jami’an tsaro su kayi wa Bukola Saraki da Ekweremadu bai dace da tsarin kasa ba – Shehu Sani

‘Dan Majalisar da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Shehu Sani yayi tir da abin da ya faru a farkon makon nan inda Jami’an tsaro su ka zagaye gidajen Shugabannin Majalisar Kasar.

Abin da Jami’an tsaro su kayi wa Bukola Saraki da Ekweremadu bai dace da tsarin kasa ba – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya soki abin da aka yi wa Bukola Saraki a gidan sa

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa kewaye gidan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kuma Mataimakin sa Ike Ekweremadu abin kunya ne kuma abin dariya. Sanatan yace an ci mutunci tsarin Damukaradiyya na Najeriya.

Jami’an ‘Yan Sanda ne ake zargi su ka zagaye gidan Bukola Saraki a shekaran jiya da safe. Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya dai tace sam babu hannun ta a wannan aiki sai dai Shugaban Majalisar kasar ne ya shirya wannan abu da kan sa.

KU KARANTA: Saraki na tunanin inda zai sa gaba bayan ya gana da Shugaban Kasa Buhari

Jami’an Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne su ka nemi shi kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan kasar Ike Ekweremadu ya mika kan sa bisa zargin facaka da wasu makudan kudi.

Sanata Shehu Sani wanda a ranar yace wasu sun shiga gidan sa su na neman say a soki wannan lamari. Sanatan wanda ya saba gwagwarmaya yace wannan danyen aiki ya batawa Gwamnati suna kuma an yi tsarin mulki karem-tsaye.

Jiya kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki yayi mursisi da gayyatar da Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya yayi masa bisa zargin sa da hannun kan laifin fashi da makami inda yace akwai lauje cikin nadi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel