Ministoci da Ma’aikatu sun dawo da Biliyan 118 cikin asusun Gwamnati

Ministoci da Ma’aikatu sun dawo da Biliyan 118 cikin asusun Gwamnati

- Gwamnatin Tarayya ta gaza kashe wasu kudi da aka ware a kasafin kudin bara

- An samu haka na a sanadiyyar bata lokacin da aka yi a kan kasafin kudin 2017

A kusan karo na farko an ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari da wasu Ministocin Kasar nan sun maido sama da Naira Biliyan 100 zuwa asusun Gwamnatin Tarayya na kudin da su kayi ragowa cikin kasafin kudin shekarar bara 2017.

Ministoci da Ma’aikatu sun dawo da Biliyan 118 cikin asusun Gwamnati

Wasu Ministoci sun dawo da canjin da ya rage daga kasafin kudin bara

Labari ya zo mana jiya cewa wasu Ministocin kasar nan sun dawo da Naira Biliyan 118 cikin asusun Gwamnati. Wannan makudan kudi dai rara ne aka samu na abin da ya kamata ace an kashe a kasafin shekarar da ta gabata watau 2017.

Akanta Janar na kasa Idris Ahmed ya bayyana wannan inda yace Ma’aikatar ayyuka da gidaje da harkar wuta ta maidowa asusun Kasar kudi har kusan Naira Biliyan 67. Haka kuma Minista Okechukwu Enelemah ya dawo da Biliyan 22.

KU KARANTA: Fayose yace akwai babbar matsala idan Buhari ya zarce

Rahoton da Ofishin Idris Ahmed ya fitar ya nuna cewa sauran Ma’aikatu irin su Ma’aiktar kudi da na kiwon lafiya da kuma Ma’ikatar ma’adanai da na harkar ruwa duk sun dawowa Gwamnatin Najeriya canjin da ya rage daga kasafin bara.

Mai bada shawara kan harkar tsaro ta maidowa Gwamnati da Biliyan 6 inda Hukumar kididdiga na kasa ta maido sama Miliyan 34. Ministan Matasa da wasnni ya maido abin da ya haura Miliyan 1. Haka kuma Ma’aikatar tsaro ta dawo da wasu kudi.

Ba dai a nan abin kurum ya tsaya ba don kuwa Ma’aikatu da dama ba su iya batar da kudin da aka ware masu ba. Hakan dai bai rasa dalili da bata lokacin da aka yi wajen sa hannu kan kasafin kudin shekarar da ta gabata da kuma farashin gangar mai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel