Mun gama yawo Idan muka bari Buhari ya maimaita mulki – Gwamna Ayo Fayose

Mun gama yawo Idan muka bari Buhari ya maimaita mulki – Gwamna Ayo Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana fargbarsa da zarcewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace sun kade idan har suka yi sake Buhari ya lashe zaben 2019, inji rahoton jaridar The Cable.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Fayose ya bayyana haka ne a ranar Talata, 24 ga watan Yuli yayin da ya kai ziyara gidajen shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ekweremadu a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Aiki ga mai kareka: Shugaba Buhari ya baiwa Sojoji sabbin jiragen yaki 30

A yayin ziyarar, Fayose ya yi Allah wadai da farkmakin da jami’an Yansanda suka kai gidajen shuwagabannin majalisar, inda yace: “Mun zo nan ne don jinjina ma karfin halinsu tare da jarumta, haka zalika muna jinjina musu sakamakon kokarin da suke yi na kwatar yancinsu daga hannun gwamnatin nan ta Azzalumai.

“Na yi tir da farmakin da Yansanda suka yi ma Ike Ekweremadu, wannan ya nuna cewa gwamnatinnan ta karaya, don haka zasu yi duk mai yiwuwa don ganin sun koma mulki, da ace haka PDP ta yi musu a zaben 2015 da basu kai labari ba,

"Ina so su sani cewa duk wani tsarin da ba Allah a cikinsa ba zai yi tasiri ba, ina kira ga Sanatoci da kada su karaya, kada su ji tsoro,su cigaba da gwagwarmaya har sai sun kwato kasarnan daga wajen azzlumai.” Inji shi.

Daga karshe Fayose yace ya zama wajibi su hada kai wajen fatattakar gwamnatin shugaban kasa Muhmmadu Buhari, inda yace: “Don haka ya zama wajibi mu hada kai kowa da kowa don korar wannan gwamnati, don kuwa idan mutuminnan ya zarce sai ya karya mana Arziki gaba daya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel