Wani Fasto ya ga ta kansa, Sojojin ruwa sun kaiwa matatar mansa sumame

Wani Fasto ya ga ta kansa, Sojojin ruwa sun kaiwa matatar mansa sumame

- Asirin wasu ma'aikatan haramtacciyar matatar man fetir ya tonu

- Tuni har sun shiga hannu Sojoji na matsar bayanai daga wurinsu

Rundunar sojin ruwan kasar nan sun bayyana cewa sun gano wani guri da ake badakalar mai wanda yake ba bisa ka'ida ba mallakin wani fasto a jihar Bayelsa.

Wani Fasto ya ga ta kansa, Sojojin ruwa sun kaiwa matatar mansa sumame

Wani Fasto ya ga ta kansa, Sojojin ruwa sun kaiwa matatar mansa sumame

Babban kwamandan daya daga cikin manyan jiragen yakin ruwan Najeriya kaftin Victor Choji ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin fatakwal a lokacin da yake holar masu laifin ga manema labarai.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa suna yiwa wani fasto wanda ba su ambaci sunansa ba aiki, tun da farko jami'an rundunar sojin ruwan sun ankara da su ne a lokacin da hankalinsu ya kai kan wani bututun Iskar gas da ya fashe.

KU KARANTA: Wani ya yiwa mahaifiyarsa yankan rago saboda ya gaji filayenta

A ranar 23 ga watan Yulin nan, jami'an sojin ruwan kasar nan dake yankin Alakiri a karamar hukumar Okirika, wadanda suke tsaka da bincike akan haramtattun matatun man da suke yankin, inda muka yi nasarar kama mutane 7 a yankin, tare da kwace danyen man da suke tacewa.

A karshe ya bayyana cewa kawo yanzu masu laifin suna tsare a hannun rundunar tsaron sojin ruwan kasar nan, don cigaba da tatsar bayanan sirri akan yadda suke gudanar da haramtattun matatun mai da ke jihohin Bayelsa da Fatakwal da yadda suke samun nasara sosai.

Ya kuma jaddada cewa babu shakka rundunarsa ba za ta zuba Ido tana ganin ana aiwatar da abubuwan da suka saba doka ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel