Wallahi ban ce Oshimhole ya zo da ‘Dan-Gashi ba – Inji Minista Amaechi

Wallahi ban ce Oshimhole ya zo da ‘Dan-Gashi ba – Inji Minista Amaechi

- Rotimi Amaechi ya musanya cewa ya soki Shugaban APC jiya

- Adams Oshiomhole ya nemi ya gyarawa wasu Ministoci zama

Wallahi ban ce Oshimhole ya zo da ‘Dan-Gashi ba – Inji Minista Amaechi

Amaechi yace bai taba cewa Oshiomhole bai zo APC da kafar sa'a ba

Mun fahimci cewa wani sabon rikici na nema ya barke a Jam’iyyar APC mai mulki bayan da Shugaban Jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole yayi barazanar korar wasu Ministocin kasar daga Jam’iyyar saboda sabawa Buhari.

A dalilin barazanar da APC tayi wa wasu Ministocin Kasar ne ake zargin cewa Rotimi Amaechi ya kira sabon Shugaban APC Adams Oshiomhole da mai ‘dan gashi. Ministan Sufurin kasar ya karyata wannan magana da ke yawo.

KU KARANTA: Jikan tsohon Shugaban kasa Shagari ya zama Shugaban Matasan Najeriya

Kalaman Adams Oshiomhole na cewa wasu Ministocin kasar sun raina Shugaban kasar bai yi wa Buhari dadi ba. Vanguard tace hakan kuma ya jawo bacin ran wasu Ministoci. Sai dai Ministan yada labarai yace za a sasanta sabanin.

Rotimi Amaechi ya bayyanawa manema labarai cewa babu wani rikici tsakanin su da shugaban APC. Kwamared Oshiomhole ya nemi Ministan kwadago Chris Ngige ya nada shugabannin wata Ma’aikata ne ko ayi waje da shi daga APC.

Amaechi yace karya kurum ake yi masa don shi ma jita-jita ya ji. Ministan yace sam bai taba sukan sabon shugaban na APC ba. Oshiomhole ya nemi a kaddamar da shugabannin Hukumar NSITF ko kuma ya sallami Ngige daga Jam’iyya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel