Aiki ga mai kareka: Shugaba Buhari ya baiwa Sojoji sabbin jiragen yaki 30

Aiki ga mai kareka: Shugaba Buhari ya baiwa Sojoji sabbin jiragen yaki 30

A kokarinsa na gamawa da kungiyar ta’addanci da sauran miyagun mutane, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sayo jiragen yaki guda dai dai har goma sha takwas, kamar yadda babban hafsan rundunar Sojan sama, Saddique Abubakar ya tabbatar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli a yayin wata ziyara da ya kai ma gwamnan jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari a fadar gwamnatin jihar dake garin Gusau.

KU KARANTA: Karshen alewa kasa: Dubun wani attajirin Kano dake luwadi da kananan Yara ta cika

Abubakar yace tun bayan hawansa kujerar shugaban kasa a shekarar 2015, Buhari ya siyo ma rundunar sojin sama sabbin jiragen yaki guda sha takwas, sa’annan ya gyara musu guda goma sha uku, wanda hakan ya kai jimillan jiragen da Buhari ya basu zuwa Talatin.

Aiki ga mai kareka: Shugaba Buhari ya baiwa Sojoji sabbin jiragen yaki 30

Saddique

“Bayan sabbin jirage 18 da ya siyo mana, ya gyara mana guda 13, kuma a yanzu muna tsimayin zuwan wasu sabbin jiragen daga kasar Amurka. Mun zo jihar Zamfara ne don ganin yadda aikin Sojan sama yake tafiya, tare da duba yiwuwar inganta aikin.

“Baya ga Sojojinmu da shelkwatan tsaro ta aika dasu jihar Zamfara, ni ma na bada umarnin turo karin wasu dakarun Sojin namu don magance ayyukan yan bindiga a jihar.” Inji shi.

Daga karshe ABubakar ya jinjina ma al’ummar jihar Zamfara, tare da gode musu bisa gudunmuwar da suke baiwa hukumar Soji, sa’annan ya kara kira garesu da su cigaba da tsegumta ma Sojoji sahihan bayanai da zasu taimaka musu wajen gudanar da aikin tabbatar da tsaro.

A nasa jawabin, gwamnan jihar, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Ibrahim Wakkala ya yaba da ayyukan rundunar Sojan sama, inda yace gwamnati za ta basu dukkan gudunmuwar da suke bukata, amma ya yi kira a garesu da su kara zage damtse.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel