Abinda ya sanya Hukumar 'yan sanda ta bukaci na gabatar da kaina - Saraki

Abinda ya sanya Hukumar 'yan sanda ta bukaci na gabatar da kaina - Saraki

A ranar Litinin din da ta gabata ne Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris, ya gayyaci Saraki domin gabatar da kansa gaban hukumar a reshen ta dake garin Guzape domin amsa wasu tambayoyi dangane da sanya hannun sa cikin aukuwar fashi da makami na garin Offa.

Saraki dai ya bayyana cewa bayan dogon nazari da hange, musabbabin wannan gayyata ba ta wuci kulla tuggu da makekashiyar cimma burika da manufofi na siyasa.

Yake cewa, ya na da tabbaci tuni hukumar 'yan sanda ta yanke shawarar gurfanar da 'yan ta'addan da suka aikata fashi da makami a bankin na Offa dake jihar Kwara. "Saboda haka neman gabatar da kansa a gaban hukumar tuggu ne domin cimma wata manufa ta siyasa."

Ya ci gaba da cewa, da silar wani tushe mai karfin gaske ya samu rahoton cewa, "gayyatar da hukumar 'yan sanda ta yi a gare sa wani tuggu ne da Sufeto Janar ya kulla domin dakile shirin wasu sanatoci da 'yan majalisar wakilai na ficewa daga jam'iyyar APC."

Abinda ya sanya Hukumar 'yan sanda ta bukaci na gabatar da kaina - Saraki

Abinda ya sanya Hukumar 'yan sanda ta bukaci na gabatar da kaina - Saraki
Source: Depositphotos

Hakazalika ya samu rahoton cewa, "muddin aka hukumar 'yan sandan ta tsare sa a tsakanin ranar Talata da Larabar da ta gabata, zai kawo karshen shirin 'yan majalisar na ficewa daga jam'iyyar."

Saraki ya kara da cewa, "hukumar 'yan sanda ta dauki wani salo na rashin gaskiya gami da yaudara tare da jefa siyasa cikin takaddamar fashin Offa. Sun mayar da wannan takaddama a matsayi wata hanya ta barazana ga masu adawa da jam'iyyar APC da hakan zai yi ma ta babban lahani a zabe mai gabatowa."

KARANTA KUMA: Saraki ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Hukumar 'Yan sanda

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Saraki dai ya bayyana cewa ko kusa ba ya da hannu cikin aukuwar fashin Offa da duk wani nau'in ta'addanci makamacin sa.

A daren ranar Larabar da ta gabata ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da sanatocin jam'iyyar APC a fadar sa ta Villa, sai dai shugaban majalisar ta dattawa bai halarci wannan ganawa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel