An tasa keyar Dino Melaye kotu, saboda yayi kokarin hallaka kansa

An tasa keyar Dino Melaye kotu, saboda yayi kokarin hallaka kansa

- A ranar Laraba ne wata kotu dake zamanta a Abuja ta yankewa wa Sanata Dino Malaye tara

- Wanda ake zargin ya aikata laifukan ne a 24 ga watan Afrilun daya gabata

- Yayi kokarin hallaka kansa, wanda faruwar hakan zai zanyowa yan sandan shiga hatsari

An tasa keyar Dino Melaye kotu, laifinsa wai yayi kokain hallaka kansa

An tasa keyar Dino Melaye kotu, laifinsa wai yayi kokain hallaka kansa

A ranar Laraba ne wata kotu dake zamanta a Abuja ta yankewa Sanata Dino Malaye tara bisa laifin daukar makami zai kashe kansa, kokarin kubucewa daga hannun yan sanda da kuma lalata wasu kayan aikin su.

Dr Alex Izonyi ya bayyanawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifukan ne a 24 ga watan Afrilun daya gabata.

Izonyi ya kara da cewa a yayin da suke kan hanyar su ta mika Malaye zuwa Lokoja a cikin motar yan sanda yayi kokarin neman hanyar tsira.

DUBA WANNAN: Minista ya shiga tsaka mai wuya

Bayan ya samu nasarar ficewa daga motar ya zauna a kasa inda yake dauke da makami yana kokarin kashe kansa wanda hakan ka iya jefa yan sandan cikin matsala.

Malaye yayiwa yan sandan barna ta hanyar fasa gilashin motar da gwiwar hannunsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel