Motocin Takumbo na bata yanayin kasashe irin su Najeriya - Bincike

Motocin Takumbo na bata yanayin kasashe irin su Najeriya - Bincike

Tsofaffin ababen hawan da ya kamata a maida su kamfanoni domin kara amfana da wasu bangarorin su kamar yanda doka ta tanadar, ana kaisu kasashen masu habakowa ne, inda suke taka rawar gani gurin samar da iskar gas da ke iya kawo dumamar yanayi

Motocin Takumbo na bata yanayin kasashe irin su Najeriya - Bincike

Motocin Takumbo na bata yanayin kasashe irin su Najeriya - Bincike

Kasashen Nahiyar Afirka da kudancin Asia bazasu iya kawo karshen iskar gas dake haddasa dumamar yanayi ba, ba tare da kasashe masu tattalin arziki sun dena maida nahiyoyin gurin zubar da miliyoyin tsofaffin ababen hawa ba, wani bincike ya ja kunne.

CSE ta ruwaito cewa US, Japan da kasashen hadin kan turai sun dau shekaru suna zubar da tsofaffin ababen hawa a kasashe irin su Najeriya da Bangladesh.

Tsofaffin ababen hawan da ya kamata a maida su kamfanoni domin kara amfana da wasu bangarorin su kamar yanda doka ta tanadar, ana kaisu kasashen masu habakowa ne, inda suke taka rawar gani gurin samar da iskar gas da ke iya kawo dumamar yanayi.

Idan ba a tsayar da hakan ba, ta hanyar hana shigo da tsofaffin ababen hawan, kasashen marasa tattalin arziki bazasu samu damar samun muhalli mai tsafta ba. Inji Anumita Rovchowdhury ta CSE a wani taron manema labarai na Facebook.

DUBA WANNAN: Kudaden da aka kashe kan Air Nigeriya ya zuwa yanzu

Akwai kusan ababen hawa biliyan 2 a duniya, kashi biyu a ciki (miliyan 40) daga ciki basu cancanci ayi amfani dasu a kasashe masu tattalin arziki ba. Da yawa daga cikin su na karewa a kasashe irin su Kenya, Najeriya da Etofia.

Kashi 90 cikin dari na motocin Najeriya an shigo dasu ne daga kasashen waje, wanda duk na hannu ne.

Wadannan motocin da yawa daga ciki sassan su basa aiki yanda ya dace, suna daukar zafi da yawa, inda suke fitar da iskar gas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel