Gwamnatin Najeriya ta antaya biliyan uku kan harkar jiragen sama na Nigerian Air

Gwamnatin Najeriya ta antaya biliyan uku kan harkar jiragen sama na Nigerian Air

- Gwamnatin tarayya zata zuba Naira biliyan 3.168 a matsayin jarin kamfanin jiragen saman Najeriya

- Shirye shiryen suna daga cikin Outline Business Case wanda Infrastructure Concession Regulatory Commission tasa hannu kafin sa hannun hukumar zababbu ta Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta antaya biliyan uku kan harkar jiragen sama na Nigerian Air

Gwamnatin Najeriya ta antaya biliyan uku kan harkar jiragen sama na Nigerian Air

Gwamnatin tarayya zata zuba Naira biliyan 3.168 a matsayin jarin kamfanin jiragen saman Najeriya.

Shirye shiryen suna daga cikin Outline Business Case wanda Infrastructure Concession Regulatory Commission tasa hannu kafin sa hannun hukumar zababbu ta Najeriya.

A yanzu dai, ana bada shawara game da daukar nauyin da gwamnati tace zatayi na kamfanin jiragen saman, gara ya zama kamfani mai zaman kanshi da zai iya gogayya da sauran kamfanonin jiragen sama.

Majiyar mu tace kudin farko, Naira biliyan 3.2 na daga cikin kashi biyar bisa dari na hannun jarin da gwamnati zata zuba, wanda zai jawo Naira biliyan 108 a shekaru 3 masu zuwa.

DUBA WANNAN: Minista ya shiga tsaka mai wuya

Majiyar mu ta ma'aikatar sufuri tace dala miliyan 300 ne mafi karantar kudin da gwamnati da yan kasuwa zasu zuba, wanda kashi biyar ne daga ciki zai zamo na gwamnati.

Daraktan ya bayyana cewa gwamnati bazata dau nauyin duka aikin ba, amma ita zata fara zuba hannun jari . Amma OBC tace akwai bukatar dama gwamnati ta fara zuba hannun jari don ganin kankamar aikin kafin yan kasuwa su shigo ciki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel