Wani Ministan gwamnati ya shiga tsaka mai wuya kan kudin Otal

Wani Ministan gwamnati ya shiga tsaka mai wuya kan kudin Otal

- Ministan siye da siyarwa da hannun jari, Okechukwu Enelamah, na da hannu a alawus kashi biyu na gurin kwana na Naira 993,000,inji rahoton mai bada bayanin kudi na Gwamnatin tarayya na 2016

- Bayanin ya nuna cewa biyan mai rikitarwa, anyi shi ne ga ministan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabe shi a matsayin minista

Wani Ministan gwamnati ya shiga tsaka mai wuya kan kudin Otal

Wani Ministan gwamnati ya shiga tsaka mai wuya kan kudin Otal

Rahoton da ya kunshi bayanin kudaden ma'aikatun gwamnatin tarayya, bangarori da cibiyoyi, daga ofishin mai bada bayanin kudi na Gwamnatin tarayya. An saki rahoton ne a watan da ya gabata.

Bayanin rahoton ya nuna cewa an biya Naira 993,195 ga wani otal a Maitama Abuja domin masauki da ciyarwa na ministan na kwanakin farkon shi a matsayin ministan.

Bayanin kudin ya kara nuna cewa an biya ministan Naira 980,000 a farkon mulkin shi a matsayin alawus na masaukin otal.

Babban mai bada bayanin kan kudin ya nuna bacin ranshi game da kudi kashi biyun da aka biya kuma ya umarci sakataren gwamnatin ma'aikatar siye da siyarwa da ta dawo da kudin da aka biya Mista Enelamah tare da bada bayanin yanda aka dawo da kudin

DUBA WANNAN:

A lokacin da majiyar mu taso Jin ta bakin Bisi Daniel, mai bada shawarar tsari da labarai na ma'aikatar siye da siyarwa da hannun jari, yace ma'aikatar tana dai bincike akan wannan biyan mai rikitarwa.

"An samu cakudedeniya ne, da kuma kamar biyan na biyu ba ma'aikatar mu aka turo ma wa ba"

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel