Saraki ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Hukumar 'Yan sanda

Saraki ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Hukumar 'Yan sanda

Legit.ng ta samu rahoton cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya yi watsi da amsa kiran sufeto janar na 'yan sanda dangane da badakalar fashi da makamin da ya afku a wani banki dake garin Offa na jihar Kwara.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, hukumar 'yan sandan ta nemi Saraki ya gabatar da kansa a shiyarta dake garin Guzape a babban birnin kasar nan domin amsa wasu tambayoyi dangane da afkuwar fashin garin Offa.

A jiya Laraba Shugaban majalisar ya bayyana cewa, bai amsa gayyatar hukumar 'yan sanda ba a karan kansa, sai dai ya bayar da amsoshin duk wasu tamboyoyi da hukumar ta gabatar cikin rubutacciyar wasikar da ta aiko a gare sa.

Saraki ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Hukumar 'Yan sanda

Saraki ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Hukumar 'Yan sanda

Saraki wanda ya fayyace dalilan da sanadin hadimin sa na musamman kan hulda da manema labarai, Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa, cikin rubutacciyar wasika Saraki ya bayar da amsar dukkanin al'amurra da tambayoyi da hukumar ta bukata.

KARANTA KUMA: Ya kamata mu raba Gari da Saraki - Kakakin Jam'iyyar APC

Yake cewa, an rubuta wasikar kuma an aika ta ga hukumar 'yan sanda a ranar Talatar da ta gabata.

Olaniyonu ya ci gaba da cewa, bayan zayyanawa hukumar 'yan sandan masaniyar sa dangane da al'amurra da tambaoyoyi da ta shinfida, sai ya fahimci babu sauran wata bukata ta bayyana a gaban ta a karan kansa.

Shugaban Majalisar ya kara da cewa, yana da cikakken yakini na wasikar sa kadai ta wadatar ba tare da wata bukata ta gabatar da kansa a gaban hukumar ba da a cewar sa aiwatar da hakan zai kasance maimai na sakonnin da riga da bayyana ma ta cikin wasikar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel