Masu garkuwa da mutane sun saki wasu jagororin APC da suka sace

Masu garkuwa da mutane sun saki wasu jagororin APC da suka sace

Wasu jagororin jam’iyyar APC uku; John Enebeli, Austin Enebeli da Afam Onyia, da masu garkuwa suka sace a karshen sati a jihar Ribas, sun samu rabauta a yau, Laraba.

An sace mutanen ne a karshen satin da ya wuce a kan hanyar Elele-Omoku ta jihar Ribas kuma sun samu ‘yancinsu a yau, Laraba. Saidai ba a bayyana yadda mutanen suka samu ‘yanci ba.

Saidai kakakin ‘yan sanda a jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya ce jami’an ‘yan sanda ne suka matsawa masu garkuwar, yayin da yake tabbatar da sakin mutanen ga manema labarai.

Masu garkuwa da mutane sun saki wasu jagororin APC da suka sace

Shugaban jam'iyyar APC; Adams Oshiomhole

Omoni ya kara da cewa, “matsin lambar da jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yiwa masu garkuwa da mutanen ne ya saka su sakin ‘yan siyasar ba tare da an biya kudin fansa ba.”

DUBA WANNAN: An yi nasarar kashe wutar da wasu suka cinna wa wani masallaci

Sakataren yada labaran APC a jihar Ribas, Chris Finebone, ya bayyana godiyarsu ga ubangiji bisa sakin jagororin nasu tare da bayyana cewar yanzu haka ana cigaba da duba lafiyar su bayan firgicin da suka shiga sakamakon hakin da suka shiga.

Kazalika ya mika godiya ga jagoran jam’iyyar APC a jihar, Rotimi Amaechi, da kuma zababben shugaban jam’iyyar APC a jihar, Honarabul Ojukaye Flag-Amachree, bisa gudunmawar da suka bayar wajen ganin an sako mutanen, da masu garkuwar suka sace, cikin koshin lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel