Kin amsa gayyatar mu rashin girmama hukuma ne - Hukumar 'yan sanda ta fadawa Saraki

Kin amsa gayyatar mu rashin girmama hukuma ne - Hukumar 'yan sanda ta fadawa Saraki

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayyan rashin amsa gayyatar hukumar da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya yi a matsayin rashin girmama hukuma.

Sufeta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya aike da wasika zuwa ga shugaban majalisa Bukola Saraki inda ya bukaci ya gurfana a ofishin hukumar don amsa wasu tambayoyi masu alaka da fashin bankuna da akayi a Offa.

Mutane biyar da 'yan sanda ta kama da ake zargi da hannu cikin fashin sun ambacin sunan Bukola Saraki.

An bukaci shugaban majalisar dattawan ya bayyana a ofishin hukumar dake Guzape a Abuje a jiya Talata misalin karfe 8 na safe amma bai amsa gayyatar ba.

Kin amsa gayyatar mu rashin girmama hukuma ne - Hukumar 'yan sanda ta fadawa Saraki

Kin amsa gayyatar mu rashin girmama hukuma ne - Hukumar 'yan sanda ta fadawa Saraki

DUBA WANNAN: Ekweremadu ya yi kunnen uwar shegu da gayyatar EFCC

A maimakon amsa gayyatar wasu jami'an 'yan sanda sun mamaye gidan Bukola Saraki a jiya amma hukumar 'yan sandan tace bata da hannu cikin lamarin.

Hukumar 'yan sandan tace tana bincike game da 'yan sandan da suka mamaye gidan shugaban majalisar inda suka kara da cewa sun karbi bayyanai daga jami'in tsaron Saraki kuma suna gudanar da bincike a yanzu.

Hukumar 'yan sandan tace an mamaye gidan shugaban majalisar ne kawai saboda a shafawa hukumar kashin kaji.

Hukumar 'yan sandan kuma tace binciken da suke gudanarwa bata da wani alaka da sauyin sheka da wasu 'yan majalisa su kayi daga jam'iyyar APC zuwa wasu jam'iyoyin.

Kakakin hukumar 'yan sanda, DCP Jimoh Moshood, ya yi tsokaci kan abubuwan dake faruwa tsakanin hukumar da shugaban majalisar dattawan a wata shirin hirar talabijin.

Moshood yace suna gayyatar Bukola Saraki ne saboda ya zo ya amsa tambayoyi game da fashin bankin da akayi a garin Offa na jihar Kwari inda aka kashe jami'an 'yan sanda da wasu fafaren hula.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel