Har yanzu muna a APC amma muna iya barinta kwanan nan – Shehu Sani da Hunkuyi

Har yanzu muna a APC amma muna iya barinta kwanan nan – Shehu Sani da Hunkuyi

Sanatocin jam’iyyar APC biyu daga jihar Kaduna, Suleiman Hunkuyi (Kaduna-Arewa) and Shehu Sani (Kaduna-Tsakiya), sun bayyana cewa har yanzu suna jam’iyyar APC amma za su barta kwanan nan.

Hunkuyi da Sani, wadda suka kasance yan kungiyar sabuwar APC sun ce zasu sanar da jama’a batun sauya shekarsu.

Akwai rade-radi da akayi tayi a ranar Juma’a cewa yan majalisan biyu wadanda ke jagorantar gamayyar kungiyar APC a Kaduna sun sauya sheka daga jam’iyar amma basu koma kowace jam’iyya ba tukuna.

Har yanzu muna a APC amma muna iya barinta kwanan nan – Shehu Sani da Hunkuyi

Har yanzu muna a APC amma muna iya barinta kwanan nan – Shehu Sani da Hunkuyi

Da yake karyata rahoton a wayar tarho, Hunkuyi yace, “Ban bari ba tukuna amma zan bari.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dalilin da ya sa na bar APC – Ortom

Dan majalisan ya bayyana cewa shi dan kungiyar R-APC ne ba APC Akida na jihar Kaduna ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel