Kotu ta daure wani saboda ya sace diyar makwabcinsa

Kotu ta daure wani saboda ya sace diyar makwabcinsa

- Wata babbar kotun majistare dake fatakwal ta bukaci da a cigaba da tsare wani mata wani mutum mai shekaru 32 a duniya da ake zargin shi da satar diyar makwafcin shi mai shekaru 2 a duniya

- Promise Okere, ya fuskanci shari'a ne da laifuka biyu kuma ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan yuni na shekarar nan a wani kauye mai suna Okujagu, a Fatakwal, jihar Rivers

- A ranar 29 ga watan yuni, 2018 a kauyen Okujagu, inda ya hada kai da wasu wajen sace yarinya. Wanda yaci karo da dashi na 516 na dokar ta'addanci na jihar Rivers

Kotu ta daure wani saboda ya sace diyar makwabcinsa

Kotu ta daure wani saboda ya sace diyar makwabcinsa
Source: UGC

Wata babbar kotun majistare dake fatakwal ta bukaci da a cigaba da tsare wani mata wani mutum mai shekaru 32 a duniya da ake zargin shi da satar diyar makwafcin shi mai shekaru 2 a duniya.

Promise Okere, ya fuskanci shari'a ne da laifuka biyu kuma ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan yuni na shekarar nan a wani kauye mai suna Okujagu, a Fatakwal, jihar Rivers.

A ranar 29 ga watan yuni, 2018 a kauyen Okujagu, inda ya hada kai da wasu wajen sace yarinya. Wanda yaci karo da dashi na 516 na dokar ta'addanci na jihar Rivers.

An hana belin wanda ake zargin amma alkalin da ke sauraron karar ya tura karar zuwa Daraktan dake kula da kararrakin jama'a domin shawarar shari'a.

Da farko, yayan yarinyar da ake kara, Dan shekaru 7 ya sanar da kotun cewa, ranar da abun ya faru, wanda ake zargi yazo har dakinsu lokacin mahaifiyar su bata nan.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya umarce mu da mu bude kofa, inda ya aikeni in siyo mata biskit, zai kula da kanwata. Amma da na dawo, banga kanwata ba.

DUBA WANNAN: Larabawa basu taimakon Falastinawa - Amurka

Na fadawa wani mai aiki a gaban gidanmu, kuma na sanar dashi yanda mukayi da makwafcin mu.

Makwaftansu ma sun shaida cewa suna wanda ake zargin da wani mutum da basu sani ba a wani gidan cin abinci dake kusa dasu.

Mai shari'ar dai ya bukaci da a cigaba da tsare wanda ake zargin inda ya daga sauraron karar zuwa 15 ga watan Augusta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel