An yi nasarar kashe wutar da wasu suka cinna wa wani masallaci

An yi nasarar kashe wutar da wasu suka cinna wa wani masallaci

An yi nasarar kashe wata wutar dare da ake zargin wasu batagari da cinna wa a wani masallaci dake birnin Durban na Afrika ta kudu.

An wayi gari ne an ga masallacin na Masjid-e-Mukhtar dake unguwar Croftdene a birnin na Durban na cid a wuta, saidai an yi nasarar kasha wutar tare da sanar da jami’an ‘yan sanda. In da bad a wani bata lokaci ba suka isa masallacin.

An yi nasarar kashe wutar da wasu suka cinna wa wani masallaci

Hasumiyar masallaci

Saleem Adam, babban limamin masallacin, ya shaidawa wata kafar yada labarai (Times Live) cewar mutanen da suka fara isa masallacin yayin da wutar ta fara ci, sun hangi wasu matasa uku na tsallaka katangar masallacin domin tserewa, kamar yadda wakilin jaridar ta Times Live ya wallafa a wani rahoto.

Ya zuwa yanzu babu wani rahoto dangane da dalilin cinna wuta a masallacin duk da kasancewar an sha kai hare-hare a masallatai a kasar.

DUBA WANNAN: Wani limami ya saki matarsa bayan ta zamma annabiya a Coci

Ko a watan Mayu saida aka taba kashe wani mutum yayin wani harin wuka da aka wani masallaci dake garin Verulum mai nisan kilomita 30 daga birnin Durban.

Kazalika a watan Yuni ma an kara kasha wasu mutane biyu yayin wani harin da aka kai na wuka a masallaci dake kusa da birnin Cape Town.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel