Abinda ka shuka: An yanke wa mutane 2 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe wani babban malami

Abinda ka shuka: An yanke wa mutane 2 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe wani babban malami

- Wasu rikakkun 'yan fashi sun samu hukunci daidai da laifin da suke aikatawa

- Asirinsu ya tunu ne bayan da suka kashe wani babban malayin addinin Kirista

- Sai dai kash wasu daga cikinsu sun tsere da suka ji labarin an kama sauran

Yanzu haka dai wasu mutane biyu sun fuskanci hukunci mai tsauri daga alkalin babbar kotun jihar Makurdi sakamakon aikata laifin kisan wani babban malamin addinin Kirista Rev. Fr Alexandra Adeyi.

Abinda ka shuka: An yanke wa mutane 2 hukuncin kisa ta hanyar rataya – Duba kowanne laifin aikata

Abinda ka shuka: An yanke wa mutane 2 hukuncin kisa ta hanyar rataya – Duba kowanne laifin aikata

Mai shari’a Aondover Kakaan ya yankewa wadanda ake zargin masu suna Suleiman Goma da Haruna Idi hukuncin kisar ne ta hanyar ratayewa a jiya Laraba.

Ana dai zargin sun hada baki ne da wasu mutune biyu Saidu Abdullahi da Aliyu Garba da tuni suka tsere, mazauna yankin Orokam dake karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benuwe, inda suka kama marigayin malamin ranar 26 ga watan Afirilu.

Da yake yanke hukuncin mai shari’a Kakaan, ya ce kasancewar an samu shaidu har takwas da suka tabbatar da wadanda ake zargin sun aikata laifin ya gamsar da kotun tuhumar da take musu.

KU KARANTA: Hayaniya ta kaure yayin da kwamishinoni ‘Yan sanda 2 su ka bayyana don maye gurbin Kwamishina

Alkalin ya kuma bayyana cewa an samu masu laifin da bindigu tare da wasu layoyi da guraye a lokacin da aka kama su a dokar daji.

Sanann ya kara da cewa, guda daga cikinsu ya amsa laifin siyo bindigogin domin yin fashi da makami da garkuwa da mutane a cikin jawabinsa na wurin ‘yan sanda.

Tun farko dai dan sanda mai shigar da kara a madadin shugaban ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris, Simon Iough, ya shaidawa kotun cewa wadanda ake zargin sun sace marigayin malamin ne sannan suka kai shi zuwa dajin Okumgaga a karamar hukumar Okpokwu ta jihar, kana suka nemi kudin fansa Naira miliyan N2m.

Amma sai dai duk da an biya su har Naira miliyan N1.5m kudin fansar sun hallaka malamin sannan suka jefar da gangar jikinsa tasa a dajin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel