2019: Yan Najeriya wayayyu ne baza su zabi PDP ba – Jigon APC

2019: Yan Najeriya wayayyu ne baza su zabi PDP ba – Jigon APC

Jam’iyyar Progressives Congress (APC) ta yarda da cewar yan Najeriya a yanzu sun san gaskiya sannan ba za su zabi jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 ba.

Wani mamba na kwamintun amintattu na APC, Mista Ismael Ahmed, a bayyana hakan a yayinda ya gabata a wani shirin Channels TV a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli a Abuja.

Ya ce da izinin Allah yan Najeriya baza su yi PDP a zaben 2019 ba domin kansu a waye yake yanzu, kuma karo da dama sun nuna rashin son PDP.

2019: Yan Najeriya wayayyu ne baza su zabi PDP ba – Jigon APC

2019: Yan Najeriya wayayyu ne baza su zabi PDP ba – Jigon APC

Wannan furuci na Ahmed na zuwa ne bayan mambobin majalisar dokokin kasar da aka zaba a lemar APC sun sauya sheka zuwa PDP.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnan Benue, Ortom ya sanar da sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

Ya kuma yi watsi da hujjar day an majalisar suka bayar na cewa jam’iyyar APC na barzana ga damokradiyar Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel