Yanzu Yanzu: Dalilin da ya sa na bar APC – Ortom

Yanzu Yanzu: Dalilin da ya sa na bar APC – Ortom

A kokarinsa na kare kansa bisa dalilan da suka sanya shi komawa tsohuwar jam’iyyarsa, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom a ranar Laraba, yayi ikirarin cewa jam’iyyar APC babin jihar na ci gaba da kai masa hari.

Da yake Magana a wani taro inda anan ne ya sanar da komawarsa jam’iyyar adawa, Ortom ya kara da cewa yan majalisar dokokin jihar 10 cikin 17 da aka zaba a karkashin inuwar APC sun shirya binsa PDP.

A yanzu Ortom ya sanar da komawarsa jam’iyyar PDP, daga inda ya sauya sheka zuwa APC wanda a karkashin ta ne aka zabe shi a matsayin gwamna a 2015.

Yanzu Yanzu: Dalilin da ya sa na bar APC – Ortom

Yanzu Yanzu: Dalilin da ya sa na bar APC – Ortom

Ya kuma daura alhakin sauya shekarsa akan hukuncin matasa na hana shi tafiya Abuja a yau inda anan ya kamata ya gana da shugabannin APC.

KU KARANTA KUMA: Babu dan majalisa daga APC da ya koma PDP – Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da jita-jita

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Gwamnan yayi sanarwan ne a wani taron shugabannin kananan hukumomi da aka zaba a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli a gidan gwamnatin jihar dake Makurdi, sa’o’i kadan bayan matasa masu zanga-zanga sun hana shi tafiya Abuja don halartan taron sasanci na APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel