Sauya shekar Sanatoci, da yan majalisar wakilai ya nuna cewa gwamnatin APC bata karbu ba – Kakakin PDP

Sauya shekar Sanatoci, da yan majalisar wakilai ya nuna cewa gwamnatin APC bata karbu ba – Kakakin PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tace sauya shekar da wasu yan majalisun dokokin kasar daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka yi alamu ne dake nuna cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza.

Kola Ologbondiyan, sakataren labarai na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi ikirarin cewa sauya shekar na wasu mamabobin jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP alamu ne na cewa jam’iyyar mai mulki ta gallazawa yan Najeriya.

Ologbodiyan, wadda ya yi wannan ikirari a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli a wata hira da Channels TV ya ce PDP na farin ciki matuka da masu sauya shekar.

Ya kara da cewa PDP ta samu karbuwa a matsayin zabin yan Najeriya bayan sauya shekar yace wasu gwamnoni a jam’iyya mai mulki ma zasu dawo PDP kwanan nan.

Sauya shekar Sanatoci, da yan majalisar wakilai ya nuna cewa gwamnatin APC bata karbu ba – Kakakin PDP

Sauya shekar Sanatoci, da yan majalisar wakilai ya nuna cewa gwamnatin APC bata karbu ba – Kakakin PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata,ya ce sauya shekar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) abune da ya kwana biyu.

KU KARANTA KUMA: 2019: Bindow ya sha alwashin kawowa Buhari Adamawa

Alhaji Ata ya tabbatar da cewar sauya shekar tashi ba zai shafi jam'iyyar APC ba, sannan kuma ba zai hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje maye kujerar shi ba a karo na biyu a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel