Yanzu Yanzu: Gwamnan Benue, Ortom ya sanar da sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Gwamnan Benue, Ortom ya sanar da sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Gwamnan yayi sanarwan ne a wani taron shugabannin kananan hukumomi da aka zaba a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli a gidan gwamnatin jihar dake Makurdi, sa’o’i kadan bayan matasa masu zanga-zanga sun hana shi tafiya Abuja don halartan taron sasanci na APC.

Yanzu Yanzu: Gwamnan Benue, Ortom ya sanar da sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Gwamnan Benue, Ortom ya sanar da sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

Sanarwan na sa ya kawo karshen rade-radin da ya kwashin tsawon watanni yana yawo cewa gwamnan ya koma PDP sakamakon rashin jituwa da shugabannin jam’iyyar a jihar Benue da na kasa.

KU KARANTA KUMA: Babu dan majalisa daga APC da ya koma PDP – Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da jita-jita

Kwanaki an rahoto cewa gwamnan ya kori kaso 80 cikin 100 na mambobin majalisar sa sannan a ranar Talata a majalisar dokokin jihar Benue ta tsige kakakinta, Terkimbi Ikyange.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel