‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna

- Kwanan wasu jami'an 'yan sanda ya kare yayinda aka kai musu hari

- An samu karuwar kai hare-hare kan jam'ian tsaron kasar san musamman 'yan sanda a cikin watan nan da muke ban kwana da shi

Wasu ‘yan bindiga sun farma jami'an ‘yan sanda akan hanyar zuwa Birnin Gwari dake jihar Kaduna yayin da suke bakin aikinsu wanda hakan yayi sandin mutuwar uku daga cikinsu nan take tare da kone motar jami'an ‘yan sandan.

Assha: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna

Assha: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna

A cikin wani jawabi da shugaban ‘yan kungiyar sa ido tare da tsaro na yankin Birnin-Gwari Ibrahim Abubakar nagwari, ya shaidawa manema labari cewa lamarin ya faru ne a daidai kauyen Ladi dake karkashin karamar hukumar ta Birnin-Gwari.

Kamar yadda yake dauke a cikin jawabin ya ce "Muna jajantawa iyalan wadanda abin ya rutsa da su tare da gaisuwa ga hukumar ‘yan sanda".

KU KARANTA: An yi ram da wanda yake kerawa Barayi da 'Yan fashi bindigogi

"Muna kara kira ga jami'an tsaro da na sa kai don su kara kaimi domin kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake yi akan hanyar zuwa Birnin-Gwari da hanyar zuwa garin Funtua, da kuma dajin Kumaku".

Ya kara da cewa "Muna kira ga daukacin jama'ar dake san ganin an samar da zaman lafiya, da suyi yunkuri wajen taimakawa hukuma tare da bayar da dukkanin wasu bayanai da zasu taimaka wajen bankado sirrin masu aikata wadannan muggan laifuka".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel