Kotu ta kulle wani shugaba a PDP da wasu mutane 10 bisa kisan wani shugaban jam'iyyar

Kotu ta kulle wani shugaba a PDP da wasu mutane 10 bisa kisan wani shugaban jam'iyyar

Kotun majistare dake Legas ta bayar da umurnin garkame Ciyaman din jam'iyyar PDP na jihar Legas, Moshood Salvador da wasu mutane 10 bisa zargin laifin kashe Ciyaman din jam'iyyar na karamar hukumar Apapa, Adeniyi Aborishade.

Alkalin kotun, Mr. Oyetade Komolafe, ne ya bayar da umurnin garkame su bayan hukumar 'yan sanda ta gurfanar da Salvador da sauran mutanen bisa laifin hadin baki da kissan gilla.

Dan sanda mai gabatar da karar ya shaidawa kotu cewa an kashe Aborishade ne ranar Asabar 21 ga watan Yuli a lokacin da jam'iyyar PDP tayi taron a kauyen Igbosuku dake karamar hukumar Eti-Osa na jihar.

An gurfanar da shugaban PDP da wasu mutane 10 a jiha guda bisa kisan wani shugaban jam'iyyar

An gurfanar da shugaban PDP da wasu mutane 10 a jiha guda bisa kisan wani shugaban jam'iyyar
Source: Twitter

'Dan sandan yace Salvador da sauran mutane 10 sun aikata laifin da ya ci karo da sashi na 233 da 223 na kundin dokar masu aikata laifi na jihar Legas shekarar 2015.

KU KARANTA: Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

Wadanda ake tuhuma da laifin kisar sune Kehinde Fasasi, Rotimi Kujore, Fatai Adele, Ismaila Abiola, Amos Fawole, Victoria Falowo, Mukaila Odukoya, Oropo Isaac, Mohammed Babangida da Ugochukwu Nwoke.

Sai dai dukkansu sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsu da ita.

Hakan yasa Alkalin kotun ya bukaci a basu masauki a gidan yari yayin da yake jiran shawarwari daga Cibiyar binciken masu laifi na jihar Legas. Ya kuma daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Augustan 2018.

A farkon makon nan, kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas ya gargadi 'yan jam'iyyar PDP a jihar da su guji tayar da zaune a jihar.

A sanarwar da kakakin hukumar 'yan sanda na Legas, CSP Chike Oti, ya bayar a ranar Lahadi, yace Aborishade ya rasu ne ranar Asabar da ta gabata lokacin da fada ta kaure tsakanin magoya bayan Salvador da Kehinde Fasisi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel