Kwankwaso ya fara tattaunawa akan 2019 bayan barin APC, ya ziyarci Sule Lamido

Kwankwaso ya fara tattaunawa akan 2019 bayan barin APC, ya ziyarci Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso a ranar Talata, 24 ga watan Yuli, ya ziyarci Alhaji Sule Lamido a gidansa dake Abuja.

Kwankwaso ya kai ziyarar ne, mintuna 30 bayan ya jagoranci sanatoci 13 wajen sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki a majalisar sanatoci.

Kwankwaso da Lamido sun kasance makusantan juna yayin da suke gwamnoni a Kano da Jigawa.

Kwankwaso ya fara tattaunawa akan 2019 bayan barin APC, ya ziyarci Sule Lamido

Kwankwaso ya fara tattaunawa akan 2019 bayan barin APC, ya ziyarci Sule Lamido

Ba’a san abunda ganawar tsakanin yan siyasan biyu ya kunsa ba a lokacin wannan rahoto.

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole zai tabbatar da nasarar Buhari a 2019: Fayemi

Su duka yan siyasan guda biyu na harar kujerar shugabancin kasar a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel