Ekweremadu ya yi kunnen uwar shegu da gayyatar EFCC

Ekweremadu ya yi kunnen uwar shegu da gayyatar EFCC

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu ya ki amsa gayyatar da hukumar yaki da masu yiwa arzkin kasa zagon kasa EFCC tayi masa a jiya don amsa tambayoyi game da zargin aikata laifin rashawa.

Wata majiya daga hukumar EFCC ta shaida wa Daily Trust cewa Ekweremadu bai bayyana a ofishin hukumar ba duk da gayyatar da aka aika masa.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa jami'an tsaro daga hukumar ta EFCC sun mamaye gidan mataimakin shugaban majalisar dake Apo.

Ekweremadu ya ki amsa gayyatar hukumar 'yan sanda

Ekweremadu ya ki amsa gayyatar hukumar 'yan sanda

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

A lokacin da aka hada wannan rahoton a daren jiya, an gano cewa jami'an tsaron sun bar harabar gidan Ekweremadu duk da cewa basu kama shi ba.

Duk kokarin da akayi na tuntunbar Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ci tura saboda wayar salularsa a kashe take.

A wasikar da hukumar EFCC ta aike wa Ekweremadu a ranar 24 ga watan Yuli, an bukaci ya hallarci ofishin hukumar misalin karfe 10 na safiyar jiya.

Wasikar mai taken 'case of conspiracy, absuse of office and money laundering' na dauke da sa hannun direktan ayyuka na hukumar mai suna Mohammad Umar Abba.

Hukumar ta bayyana a wasikar cewa ya zama dole a gayyaci Ekweremadu ya amsa wasu tambayoyi saboda an ambaci sunansa cikin binciken da hukumar ke gudanarwa.

A halin yanzu an tattaro cewa hukumar EFCC tana tsamanin shugaban majalisar zai amsa gayyatar nata a nan gaba domin ya wanke kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel