An shiga jimami a jami’ar jihar Katsina bayan yan bindiga sun halaka wani dalibi

An shiga jimami a jami’ar jihar Katsina bayan yan bindiga sun halaka wani dalibi

Malamai da daliban jami’an Umaru Musa Yar’adu ta jihar Katsina sun fada halin jimami tare da alhinin mutuwar wani dalibin jami’ar mai suna Muhammad Kamaladdeen Alaka, wanda yan bindiga suka bindige shi har lahira, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun halaka Alaka ne a ranar Alhamis 19 ga watan Yuli akan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa garinsu Ilori a jihar Kwara bayan ya kammala jarabawarsa.

KU KARANTA: Yansanda sun kama Sojoji da laifin satar Turansufoma

An shiga jimami a jami’ar jihar Katsina bayan yan bindiga sun halaka wani dalibi

Alaka

Alaka ya kasance dalibi ne a tsangayar koyar da harshen turanci, kuma an shaideshi da kokari da jajircewa, inda rahotanni sun tabbatar da cewar nan take Alaka ya fadi matacce bayan yan bindiga sun saita shi a kai.

Shugaban daliban harshen Turanci na jami’a, Salahuddeen Belgore ya bayyana bacin ransa da mutuwat Alaka, inda yace: “Mun ji zafin rashin Alaka, Abokinmu kuma Abokin gwagwarmaya. Da fatan Allah ya jilkanshi”

Zuwa yanzu dai an binne Alaka a garinsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, Allah ya jikansa da gafara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel