Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

Fadar shigaban kasa ta bayyana cewa a kundin tsarin mulki Najeriya, shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da bincike da ake yiwa wani mutum ko kuma ma'aikata.

Fadar shugaban kasar tayi wannan tsokaci ne game da kaiwa da komowa da aka dade ana yi tsakanin hukumar 'yan sandan Najeriya da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, game da fashin da akayi a Offa dake jihar Kwara.

Hukumar 'yan sandan ta aike wa Saraki sammaci don ya taho ofishinta dake Guzape ya amsa tambayoyi a jihar duk da cewa fadar shugaban kasar bata ambacci sunan Saraki a cikin sanarwar da ta fitar ba.

Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari yaki amincewa da wasu dokoki 5 da majalisa ta yi

A sanarwan da ta fito daga bakin babban mataimakin shugaban kasa a fadin kafafen yadda labarai, Malam Garba Shehu, shugaban kasan ya lura cewa duk lokacin da hukumar 'yan sanda ta gayyaci wani babban mutum don ya amsa tambayoyi sai a fara amfani da wannan damar wajen sukar shugaban kasa.

"Abin mamaki ne da takaici yadda hukumomin tsaro zasu iya kiran talakawa domin amsa tambayoyi amma da zarar an gayyaci wani babban mutum a kasar sai a fara yiwa lamarin fasara mara kyau ana danganta ta da siyasa ko cin zarafi.

"Ba za mu tabba samun dawamamen zaman lafiya da cigaba ba muddin ana banbanta yadda doka ke aiki a kan talakawa da manyan mutane," inji Garba Shehu.

Fadar shugaban kasar ta kara da cewa, "Shugaba Buhari baya yiwa hukumomin tsaro katsalandan cikin ayyukansu. A karkashin kudin tsarin kasarmu, shugaban kasa bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa wani mutum ko ma'aikata.

"Abinda duk dan kasa na gari ya dace ya yi shine ya bar doka da jami'an tsaro suyi aikinsu babu tsangwama."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel