Gwamnatin tarayya za ta tursasa Ma'aikata amfani da Jiragen ta yayin sufuri

Gwamnatin tarayya za ta tursasa Ma'aikata amfani da Jiragen ta yayin sufuri

Domin samun wurin zama tare da karbuwa a kasar nan, gwamnatin tarayya a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana kudirin ta na tursasa dukkanin ma'aikatan gwamnati wajen amfani jiragen saman ta yayin jigila a lokutan da wani sufuri ya kama su.

A cewar karamin Ministan sufuri na jiragen sama, Hadi Srika, gwamnatin tarayya ta fara gudanar da shirye-shirye wajen neman amincewar majalisar tarayya domin tabbatar da wannan kudiri da cimma manufar da ta sanya a gaba.

Ministan ya kuma yi karin haske dangane da karairayi da ake yi na cewar kamfanin jiragen sama na kasa ba ya da wata manhaja ballanta sunan shafin kamfanin na yanar gizo.

Gwamnatin tarayya za ta tursasa Ma'aikata amfani da Jiragen ta yayin sufuri - Hadi Srika

Gwamnatin tarayya za ta tursasa Ma'aikata amfani da Jiragen ta yayin sufuri - Hadi Srika

Kamar yadda Ministan ya bayyana, gwamnatin tarayya za ta kaddamar da doka ta tursasa sayen tikitin jiragen ta na sama ga dukkanin ma'aikatan gwamnati da za su yi jigilar safarar su da dukiyar ta.

KARANTA KUMA: Wani tsohon Kwamishina na hankoron Kujerar Tambuwal a jihar Sakkwato

Ministan domin kawar da shakku da tuhumar da ake yi ya bayar da sunan shafin kamfanin jiragen saman na Najeriya kamar haka; www.flynigeriaair.com, tare da bayar da tabbacin kaddamar da sabon shafin a yanar gizo.

Legit.ng ta fahimci cewa, a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya da kaddamar da sabon kamfanin ta na jiragen sama mai sunan Nigeria Air da ya karawa kasar nan kima a idon duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel