Kwankwaso ya jima da sauya sheka – Kakakin majalisar Kano

Kwankwaso ya jima da sauya sheka – Kakakin majalisar Kano

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata,ya ce sauya shekar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) abune da ya kwana biyu.

Da yake hira da jaridar Daily Trust, Alhaji Ata ya tabbatar da cewar sauya shekar tashi ba zai shafi jam'iyyar APC ba, sannan kuma ba zai hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje maye kujerar shi ba a karo na biyu a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.

Kwankwaso ya jima da sauya sheka – Kakakin majalisar Kano

Kwankwaso ya jima da sauya sheka – Kakakin majalisar Kano

Ata yayi bayanin cewa nasara a komai ciki harda zabe yana a hannun Allah ne, shi ne mai ba da mulki ga duk wanda ya so a lokacin da ya so.

KU KARANTA KUMA: Za’a samu karin masu sauya sheka a majalisar wakilai – Dan majalisa

Kan rade-radin cewa wasu yan majalisan jihar sun bar APC zuwa PDP, kakakin majalisar yace a iya saninsa babu makamancin haka, cewa babu wani dan majalisar dokokin jihar Kano ko guda daya koma PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel