Jarumta: R- APC ta yabawa 'yan Majalisa da suka sauya sheka

Jarumta: R- APC ta yabawa 'yan Majalisa da suka sauya sheka

A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar nan ta R-APC karkashin babbar jam'iyyar APC, ta yabawa 'yan majalisar tarayya da suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun adawa musamman jam'iyyar nan ta PDP.

Cikin wata sanarwa da sanadin sakataren kungiyar ta R-APC, Prince Kassim Afegbua, ya yabawa 'yan majalisar tare da yi masu lakabi na jarumta dangane da wannan abin son barka da suka aikata.

Kungiyar ta kuma bayyana takaicin ta dangane da fafutikar shugaban kasa Muhammadu Buhari na dakile tare da kawo tangardar wannan yunkuri na sauyin shekar 'yan majalisar, inda jami'an tsaro suka hana shige ko fice daga gidan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da aka yiwa kawanya a ranar da ta gabata.

Jarumta: R- APC ta yabawa 'yan Majalisa da suka sauya sheka

Jarumta: R- APC ta yabawa 'yan Majalisa da suka sauya sheka

Kamar yadda shafin jaridar ta Vanguard ya bayyana, kungiyar ta R- APC tayi habaice-habaice daban-daban na bayyana takaici gami da cin kashi da ake yiwa dimokuradiyyar kasar nan tare da muzguni na rashin samun 'yanci tamkar na mulkin soji.

KARANTA KUMA: Ku kyale Hukumomin tsaro su gudanar da ayyukan su - Fadar Shugaban Kasa

Kazalika kungiyar ta bayyana takaicin ta karara dangane da gudanarwa shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, akan yadda yake gindaya umarni da tsarika tamkar wani shugaban kasa da hakan ya kasance barazana ha dimokuradiyyar kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar ta kuma mika sakon ta na godiya ga dukkanin masu ruwa da tsaki da suke ci gaba da taka rawar gani wajen fafutikar kwato 'yanci da romon dimokuradiyya a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel