Zaben Ekiti: INEC da kotun zabe na shirya min makarkashiya - Olusola

Zaben Ekiti: INEC da kotun zabe na shirya min makarkashiya - Olusola

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna da aka gudanar a Ekiti a ranar 14 ga watan Yuli, Farfesa Kolapo Olusola, ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta INEC da yi masa zagon kasa a yunkurinsa na shigar da kara a kotun karar zabe.

Olusola yaki amincewa da nasarar da dan takarar jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya yi kamar yadda INEC ta sanar a karshen zaben.

Ya yi ikirarin cewa hukumar INEC ta ki amincewa da bukatar da ya shigar na samun ainihin takardun sakamakon zaben da aka gudanar duk da cewa ya cika dukkan ka'iddojin da hukumar ta gindaya.

Zaben Ekiti: Hukumar INEC na min zagon kasa game da korafin zabe - Olusola

Zaben Ekiti: Hukumar INEC na min zagon kasa game da korafin zabe - Olusola

Ya yi kira ga kotun karar zaben ta gaggauta duba korafe-korafen da ya shigar guda biyu domin a bawa doka damar tayi aikin ta.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen Sanatocin APC da suka rage bayan ficewar wasu 15

"Mun shigar da takardan neman takardun sakamakon zaben na ainihi saboda muyi amfani dasu wajen gabatar da karar mu a gaban kotu.

"Mun shigar da bukatar samun takardun a ranar 16 ga watan Yuli ga ofishin kwamishinan zabe na Ekiti, Farfesa Abdulganiyu Raji, mun biya kudi a ranar 20 ga watan Yuli amma har yanzu INEC bata sakar mana takardun ba.

"Mun kuma shigar da bukatar mu ta neman sakamakon zaben na ainihi a ofishin shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, a ranar 17 ga watan Yuli kuma mun biya kudi a ranar 18 ga watan Yuli."

Olusola yace har yanzu ba'a bashi takardun da ya nema ba duk da cewa ya yi ta zuwa ofishin INEC dake Ekiti da kuma Abuja.

Olusola ya yi ikirarin cewa INEC tana bata masa lokaci ne saboda ya fusata kuma ya karaya kamar yadda masu gidansu suka umurce su da aikatawa.

Jami'in hulda da jama'a na INEC a jihar Ekiti, Alhaji Taiwa Gbadegesin bai amsa wayarsa ba kuma bai amsa sakon tes da wakilin Punch ya aika masa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel