Samamen jami'an tsaro: Kungiyar kiristocin Najeriya sun shigar wa Saraki da Ekweremadu

Samamen jami'an tsaro: Kungiyar kiristocin Najeriya sun shigar wa Saraki da Ekweremadu

Hadaddiyar kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya watau Christian Association of Nigeria (CAN) ta gargadi fadar shugaban kasa da sauran jami'an tsaro da cewa su bi ahankali kar su jefa demokradiyyar kasar cikin rikici.

Kungiyar dai ta bayyana hakan ne jim kadan bayan wani samame da sanyin safiyar jiya da jami'an 'yan sandan Najeriya suka kai a gidan shugabannin majalisar dattijai, Dakta Bukola Saraki da mataimakin sa Ike Ekweremadu.

Samamen jami'an tsaro: Kungiyar kiristocin Najeriya sun shigar wa Saraki da Ekweremadu

Samamen jami'an tsaro: Kungiyar kiristocin Najeriya sun shigar wa Saraki da Ekweremadu

KU KARANTA: Buhari zai sake yashe kogi a Arewa

Legit.ng ta samu a cikin takardar da CAN din ta fitar dauke da sa hannun shugaban ta Dakta Samson Olasupo Ayokunle cewa abun takaici ne yadda jami'an tsaron ke neman bari 'yan siyasa su bata masu suna.

A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi wa takwaran sa duk dai a jihar, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso maraba da dawowar sa jam'iyyar PDP tare da bayyana lamarin da cewa abun murna ne.

Sai dai kuma Shekaru din ya bayyana cewa dole ne Kwankwaso yayi biyayya ga jagororin jam'iyyar a jihar idan dai har yana so ya samu zaman lafiya da salama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel