Dalilin da ya sa muka tsige kakakin mu - Inji 'yan majalisar jihar nan ta Arewa

Dalilin da ya sa muka tsige kakakin mu - Inji 'yan majalisar jihar nan ta Arewa

'Yan majalisar dokokin jihar Benue dake a yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya sun bayyana cewa dalilin su na tsige kakakin su mai suna Terkimbi Ikyange a ranar Talatar da ta gabata shine saboda ya cika taurin kai da tsattsauran ra'ayi.

Majiyar mu dai ta ruwaito cewa tsohon kakakin majalisar dai a jiyan ne 'yan majalisa 21 a cikin 30 na jihar suka jefa kuri'ar tsige shi.

Dalilin da ya sa muka tsige kakakin mu - Inji 'yan majalisar jihar nan ta Arewa

Dalilin da ya sa muka tsige kakakin mu - Inji 'yan majalisar jihar nan ta Arewa

KU KARANTA: Ciwo ya kama wadda aka yi wa karin girman duwawu a Najeriya

Haka nan mun samu cewa tuni dai 'yan majalisar suka zabi Titus Uba domin ya maye gurbin sa.

A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi wa takwaran sa duk dai a jihar, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso maraba da dawowar sa jam'iyyar PDP tare da bayyana lamarin da cewa abun murna ne.

Sai dai kuma Shekaru din ya bayyana cewa dole ne Kwankwaso yayi biyayya ga jagororin jam'iyyar a jihar idan dai har yana so ya samu zaman lafiya da salama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel