Yayinda yan majalisa da yawa suka sauya sheka a APC, gwamnoni sun yunkura domin ceto jam’iyyar

Yayinda yan majalisa da yawa suka sauya sheka a APC, gwamnoni sun yunkura domin ceto jam’iyyar

Gwamnonin Najeriya da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za su gana a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, domin samo hanya mafi inganci don magance yawan suya shekar da ya afku a Jam’iyyar.

Wannan bayani na kunshe ne a wani rahoto daga jaridar Daily Trust, wadda rahoto wata majiya dake cewa: “Sama da gwamnoni 20 za su hallara sannan kuma suna da ajanda mai karfi wadda shine tabbatar da cewa babu tawaa a jihohi inda dukkanmu mun san cewa anan tarin matsala suke.

“Sannan kun san abubuwan da gwamnoni za su iya i, dukkansu sun fito domin ramuwar gayya saboda mafi akasarin fadan ana yin su ne a matakin jiha; babu shakka Buhari zai kayar da duk wani dantakara da PDP za ta tsayar.

Yayinda yan majalisa da yawa suka sauya sheka a APC, gwamnoni sun yunkura domin ceto jam’iyyar

Yayinda yan majalisa da yawa suka sauya sheka a APC, gwamnoni sun yunkura domin ceto jam’iyyar

“Amma dai abu mafi muhimmanci, bama hana kanmu bacci saboda duk wadanda suka koma PDP za su tarar da lamari mafi muni a chan, akwai mutanen da suka sha wahala da PDP sannan bazasu yadda a masu fin karfi ba.

“Sannan kun san me? Shi kansa Saraki yana hararar tikitin shugabancin kasa ne. Kwankwaso ma na neman tikitin sannan shin kuna ganin mutane irin su Atiku, Sule Lamido, Makarfi, Shekarau da tarin yan takarar shugaban kasa za su aiye kudirinsu ne haka kawai?

KU KARANTA KUMA: Tsohon Gwamna Kwankwaso ya raba kan ‘Yan Majalisar Kano

“Ku zuba idanu ku gani, za su yaki kansu ne gabannin zaben fid da gwani,” inji shi.

A halin yanzu, jam’iyyar APC ce ke mulkar jihohi 26 cikin 36 na tarayyar kasar, harda Ekiti da jam’iyyar ta lashe kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel