Dalilin da ya sa Bukola Saraki da Dogara ba su koma Jam’iyyar PDP ba tukun

Dalilin da ya sa Bukola Saraki da Dogara ba su koma Jam’iyyar PDP ba tukun

- Ba da dadewa ba Shugaban Majalisar Wakilai da Dattawa za su bar APC

- Shugabannin Majalisar za su sauya sheka su koma Jam’iyyar adawa PDP

- Wasu manyan ‘Yan Majalisan APC fiye da 50 sun bar Jam’iyya mai mulki

Dalilin da ya sa Bukola Saraki da Dogara ba su koma Jam’iyyar PDP ba tukun

Har yanzu Bukola Saraki da Dogara ba su bar Jam’iyyar APC ba

Mun samu labari cewa akwai babban dalilin da ya hana Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kuma Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Yakubu Dogara ficewa daga Jam’iyyar APC duk da wasun su sun tsere daga APC a zaman jiya.

Duk da cewa a jiya wasu manyan ‘Yan Majalisar kasar su ka tsere daga APC zuwa PDP, su dai Shugabannin Majalisar sun yi zaman su. Akwai ‘Yan ganin-kashe nin Dogara da Saraki da dama da yanzu sun koma Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Saraki yayi watsi da gayyatar Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya

Wani ‘Dan Majalisar Kasar ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Saraki da Dogara sun bar APC sai dai kurum lokaci ake jira yayi. Shugabannin Majalisar sun yi hakan ne domin jan lokaci su ga yadda abubuwa za su kaya a siyasar kasar.

Majiyar ta bayyana cewa ba da dadewa ba Shugabannin Majalisar Kasar da kuma wasu manyan Gwamnonin APC za su sauya sheka su koma Jam’iyyar PDP. Da alamu dai Saraki da Dogara su na daukar mataki ne sannu a hankali.

Kun ji labari cewa wasu Sanatocin da ba su goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki sun nemi su tsige sa daga kujerar sa a jiya. Sai da ba su kai ga labari ba Bukola Saraki ya farga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel