Shugaban Majalisar Dattawa yayi mursisi da gayyatar ‘Yan Sanda

Shugaban Majalisar Dattawa yayi mursisi da gayyatar ‘Yan Sanda

Da alamu dai Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki yayi mursisi da gayyatar da Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya yayi masa bisa zargin sa da hannun kan laifin fashi da makami don har yanzu bai mika kan sa ba.

Shugaban Majalisar Dattawa yayi mursisi da gayyatar ‘Yan Sanda

Saraki yayi mursisi da gayyatar ‘Yan Sandan Najeriya ya wuce Majalisa

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki bai halarci gayyatar da Sufetan’Yan Sandan Najeriya yayi masa ba. Manema labarai sun samu labari cewa Bukola Saraki bai taka kafar sa zuwa ofishin ‘Yan Sanda kamar yadda aka shirya ba har yanzu.

Jami’an ‘Yan Sandan sun gayyaci Bukola Saraki ofishin su da ke Unguwar Guzape a babban Birnin Tarayya Abuja domin ya amsa tambayoyi game da zargin sa da hannu a fashin da aka yi kwanaki a Garin Offa da ke cikin Jihar Kwara.

KU KARANTA: Har gobe APC ce da rinjaye a Majalisar Najeriya

Takardar da ‘Yan Sanda su ka aikawa Bukola Saraki ta nemi ya hallara a gaban ta ne jiya Talata da karfe 8 na safe. Sai dai duk da zagaye gidan Shugaban Sanatocin da aka yi, bai leka ofishin ‘Yan Sandan domin ya wanke kan sa ba a jiya da safen.

Kakakin ‘Yan Sandan Kasar yace DCP Jimoh Moshood yace ba a kayyade lokacin da Bukola Saraki zai kawo kan sa ba. Jami’an ‘Yan Sandan dai sun ce babu abin da zai hana su aikin su inda kuma yayi watsi da zargin cewa an zagaye gidan Sarakin.

Shekaran jiya kun ji cewa Bukola Saraki ya maida kakkausan martani bayan ‘Yan Sanda sun gayyace sa gaban su. Shugaban Majalisar yace ana neman garkame sa ne domin hana wasu ‘Yan Majalisan Kasar barin Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel