Ana zaton wuta a mekera sai ga ta a masaka: Yansanda sun kama Sojoji da laifin satar Turansufoma

Ana zaton wuta a mekera sai ga ta a masaka: Yansanda sun kama Sojoji da laifin satar Turansufoma

Jami’an rundunar Yansandan jihar Delta sun kama wasu dakarun Sojin ruwa guda Uku da laifin satar kayayyaki daga wani dandamalin ajiyan jiragen ruwa dake garin Warri, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sojojin da aka kama sun hada da Usman Shuaibu da wasu abokansa guda biyu, an kama su ne bayan sun yi kokarin satar na’urar rarraba wutar lantarki, Transformer da wani injin daure kaya.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na shiga fadar shugaban kasa sau 3 a rana daya – Babban sufetan Yansanda

Sai dai majiyar ta bayyana cewa wadannan na’urori da Sojojin suka yi kokarin sacewa mallakin tsohon shugaban tsagerun Neja Delta ne, Ekpemupolo Government Tompolo.

Kaakakin Yansandan jihar Delta, Aniamaka Andrew ya tabbatar da kama Sojojin, inda yace da ba don Yansanda sun yi hanzarin zuwa wajen da Sojojin ke satar ba da sun sha da kayan da suka sata.

“A yanzu haka dukkanin kayan da suka sata suna ajiye a ofishin Yansanda dake garin Warri, sa’annan hukumar Yansanda ta kaddamar da bincike game da lamarin.” Inji shi.

Daga karshe rundunar Yansandan jihar Delta ta bayyana cewa za ta hada kai da rundunar Sojin ruwa don gudanar da wannan bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel